Labarai
‘Yan Gida Daya Sun Rasu Bayan Cin Abincin Dare

Wasu ‘yan uwa 7 sun mutu a kauyen Danbaza da ke karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara sakamakon cin gauraye kayan lambu tare da masara.
Lamarin ya faru ne nan take bayan ’yan uwa sun dauki gauraye kayan lambu da masara da aka fi sani da (Dambu) da aka shirya a matsayin abincin dare.
Wadanda suka rasu din dai sun hada da matan aure biyu, ‘ya’ya uku da kuma jikokin gidan.
Wata majiya da ta ke kusa da ‘yan uwa, Muhammad Kabir ya ce da mutanen sun gama cin abinci, hudu daga cikin bakwai da suka rasun sun mutu nan take, yayin da uku kuma aka garzaya da su asibiti amma kuma sun mutu a can kuma an mayar da su gida don yi musu jana’iza.
Da yake jajantawa ‘yan uwan a garin Danbaza, Kwamishinan yada labarai Ibrahim Dosara ya bayyana rasuwar ‘yan uwa guda bakwai a matsayin abin takaici, sannan ya yi addu’ar Allah Subhanahu Wata’ala ya baiwa mamatan Aljannar Firdausi da iyalansa hakurin jure rashin da ba za a iya misaltawa ba.
Ya kuma shawarci al’ummar jihar da su rika kula da abin da suke ci da kuma yadda suke shirya abincinsu kafin a ci abincin.
Da yake mayar da martani a madadin iyalan, Malam Hassan Danbaza ya ce ya rasa matansa biyu da ‘ya’yansa uku da jikoki biyu a lamarin.
Radio Nigeria/Nigeriantracker