Connect with us

Labarai

Gwamnan Borno Ya Amince Da Mafi Karancin Albashin Ma’aikata A Jihar

 

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya amince da aiwatar da mafi karancin albashi na Naira 30,000 ga kwararrun malamai 4,491 a karkashin tsarin albashin ma’aikatan kananan hukumomin jihar daga ranar 1 ga watan Agusta, 2022.

KAKAKIHAUSA ta rawaito cewa, Idai za a iya tunawa gwamnatin jihar a karkashin jagorancin Gwamna Zulum ta fuskanci tuhuma a kafafen sada zumunta a makon da ya gabata cewa malaman da ke aiki da makarantun firamare na karbar albashi a wata-wata tsakanin Naira 7,000 zuwa Naira 11,000 a matsayin albashin su.

Gwamna Babagana Zulum wanda ya dawo daga kasar Japan bayan wata ganawa da ya yi a hukumance ya amince lokacin da yake ganawa da shuwagabannin hukumar da ma’aikatan gwamnati da na kananan hukumomi da shugaban ma’aikata da kuma mambobin kungiyar malamai ta Najeriya NUT. da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC a gidan gwamnati dake Maiduguri ranar Laraba.

Zulum ya kuma bayar da tabbacin cewa za a fara aiwatar da ci gaban karin girma ga daukacin ma’aikatan jihar daga watan Janairun 2022 zuwa 2023 bayan an gudanar da jarrabawar karin girma, yana mai jaddada cewa idan jihar Yobe za ta iya yin jarrabawar karin girman, me zai hana Borno yin hakan.

” Matsalolin da ke faruwa a ma’aikatan gwamnati da na kananan hukumomi suna da yawa. Mutane da yawa sun kasa fahimtar matsalolin da muke fukanta, amma ina tabbatar muku za mu zauna mu magance su cikin lokaci,” in ji shi.

Ya koka da cewa kimanin malamai 3,000 da ke karban albashin a jihar ba su da wata kwakkwarar takaddar shedar fanni koyarwa, amma ya ba da tabbacin cewa za a horar da wadanda suka cancanta.

“Za mu dauki malamai 1000 da za a basu horo su a kwalejojin ilimi Biu da Bama, yayin da za a horar da wasu tare da hadin gwiwar cibiyoyin malamai na kasa (NTI) na tsawon watanni 6, idan suka ci jarrabawar za a sa su cikin tsarin”, ya kara jaddada.

Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Tun da farko, Shugaban kungiyar NLC na jihar Borno, Kwamared Yusuf Inuwa ya yabawa Gwamna Zulum bisa biyan hakkokin ma’aikatan na shekarar 2020, tare da ba shi tabbacin cewa kungiyar na ci gaba da bai wa gwamnatinsa hadin kai da goyon bayan masana’antu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet