Labarai
Kaduna: An cafke mutane 7 da ake zargin ƴan bindiga ne

Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da cafke wasu mutane bakwai da ake zargin ƴan bindiga ne a ƙauyen Mariri da ke yankin ƙaramar hukumar Lere ta jihar.
Hakan na cikin sanarwar da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya fitar da da yammacin Larabar makon nan.
Sanarwar ta ce an kama mutanen ne bayan samun bayanan sirri a kansu
Haka kuma sanarwar ta ce, dakarun Operation Safe Haven ne suka kama mutanen Musa Adamu da Abdullahi Usman da Suleiman Hasidu sai Usman Jibril da Saidu Isah da Hassan Abdulhamid da kuma Idris Sani.