Featured
Ganduje ya bada umarnin mayar da wajen da ginin Beirut ya rushe zuwa wajen fakin

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bada umarnin mayar da wurin da gini ya rufta a kasuwar sayar da wayoyi ta Beruit zuwa filin a jiye ababen hawa.
Gwamna Ganduje ya furta hakan ne lokacin da ya kai ziyarar jaje wurin da iftila’in ya faru da yammacin yau Laraba.
Haka kuma ya ce, gwamnatinsa ba za ta yarda a sake yin gini a wurin ba bisa yadda wurin yake.