Connect with us

Labarai

Wike Ya Zargi Buhari Da Amaechi Da Katsalandan A Zaben Jihar Rivers

Gwamna Nyesom Wike ya zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi da yin katsalandan a zaben gwamna na 2019 a jihar Ribas.

Gwamna Wike ya yi wannan ikirarin ne a ranar Larabar nan yayin bikin kaddamar da aikin gina titunan cikin gida a garin Igwuruta da ke karamar hukumar Ikwerre ta jihar.

Ya ce shugaban kasar ta bakin tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya yi amfani da jami’an tsaro wajen yunkurin murde zaben gwamnan.

Jaridar Daily Post ta rawaito cewa Gwamnan ya ce al’ummar jihar sun yi watsi da matakin da hukumomin tsaro suka dauka.

Ya ce “Na ji Mista shugaban kasar ya fada jiya cewa ba zai tsoma baki ba (a zaben 2023). Ya shaida wa gwamnoni ba zai tsoma baki ba.

“A daya (2019) kun tsoma baki tare da turo mutane su zo su karasa mu a jihar Ribas.

“Na gode shugaban kasa da cewa ba za ku tsoma baki ko tsoratar da kowa ba. Ma’ana babu wata hanya ga jam’iyyar ku.

“Tabbas ya tsoma baki a karon karshe ta hanyar amfani da sojoji ta hannun tsohon ministan sufuri amma jama’a suka tashi suka ce a’a hakan ba zai faru ba.

“Na gode wa shugaban kasa da ya ke son barin a gudanar da zabe na gaskiya da adalci”.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet