Labarai
Ƙungiyoyin kishin al’umma sun soki naɗin da Buhari ya yi wa yayan matarsa

Wasu ƙungiyoyin rajin kare haƙƙin ɗan adam a Najeriya, tare da ƙungiyar ma rubuta kan harkokin ƴan mutane watau HURIWA, sun soki naɗin da shugaba Buhari ya yi wa yayan matarsa Ahmed Halilu a matsayin shugaban kamfanin buga kuɗi NSPMC.
A cewar ƙungiyar HURIWA shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya karya alƙawarin da ya yi lokacin da za’a raantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa inda ya ce, ba zai yi son rai ba wajen gudanar da mulkinsa.
Haka kuma ta ƙara da cewa akwai lauje cikin baɗi dangane da bai wa yayan Aisha Buhari wannan babban muƙami.