Connect with us

Labarai

An Saki Shugaban Karamar Hukumar Da Aka Yi Garkuwa Da Shi

Bayan sace shugaban karamar hukumar Kanke ta jihar Filato, Honarabul Henry Jan Gotip, an sake shi.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Filato, DSP Alabo Alfred, ya tabbatar wa manema labarai sakin wanda aka sace din, ya kuma kara da cewa an sako Henry ba tare da jin rauni ba a daren ranar Larabar nan.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda aka yi garkuwa da shugaban karamar hukumar a ranar Larabar nan, a gidansa da ke karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar.

Alfred ya ce, “Shugaban karamar hukumar ya sake haduwa da iyalansa kuma nan ba da dadewa ba rundunar ‘yan sandan da ke yaki da masu garkuwa da mutane za ta tattauna da shi domin samar da bayanan sirri da za su kai ga cafke wadanda suka sace shi.

“Kwamishanan ‘yan sanda na jihar Filato, CP Bartholomew N. Onyeka, ya nanata kudurin rundunar na mai da jihar mai zaman lafiya ga daukacin mazauna Filato. Ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da taimaka wa ‘yan sanda da bayanan da suka dace domin su ba su damar mayar da martani cikin gaggawa kan aukuwar wani lamari.”

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahistipobettipobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişjojobetjojobetgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobettipobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet