Labarai
Wabara Ya Maye Gurbin Walid Jibril A Matsayin Shugaban BoT Na Jam’iyyar PDP

Tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Adolphus Wabara, ya zama sabon shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP.
Nadin nasa ya biyo bayan murabus din da tsohon shugaban kwamitin na jam’iyyar PDP na kasa, Walid Jibril ya yi, a daidai lokacin da rikicin da ya dabaibaye babbar jam’iyyar adawa a kasar.
An sanar da murabus din Jibril da nadin Wabara ne a ranar Alhamis din nan a taron BoT da na kwamitin majalisar zartarwa na kasa ranar Alhamis din nan a Abuja.
Channels TV