Labarai
Ana Fargabar Mutane 13 Sun Rasa Ransu A Jihar Jigawa

Mutane 13 ne ake fargabar sun mutu a wani hatsarin kwale-kwale a karamar hukumar Ringim ta jihar Jigawa.
Rahotanni sun ce lamarin ya afku ne da yammacin ranar Lahadi lokacin da fasinjojin suka shiga cikin wani kwale-kwale daga kauyen Dabi zuwa Sayango domin jajantawa iyalansu kan rasuwar wani dan uwansu.
Wasu daga cikin wadanda hatsarin ya rutsa da su an samu nasarar ceto su, yayin da wasu kuma ba a gansu ba.
Kakakin rundunar ‘yan sandan DSP Lawan Shiisu Adam ya tabbatar wa DAILY POST faruwar lamarin.