Labarai
Hotuna Masu Magana, Ana Zargin An Raba Wasu Miliyoyin Naira A Majalisar Shura

Hotuna sun nuna wasu mambobin Shura, majalisar shawara ta harkar siyasar Sanata Ibrahim Shekarau, suna raba wani kaso na Naira miliyan 100 da ake zargin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayar domin tara magoya bayan jam’iyyar a ziyarar da ya kawo Kano.
Masu bincike sun shaidawa Jaridar DAILY NIGERIAN cewa dan takarar shugaban kasa ya yiwa shugabannin PDP na Kano naira miliyan 130, inda Malam Shekarau ya samu kaso na naira miliyan 100, sansanin Aminu Wali ya samu Naira miliyan 30.
A karshen watan Agusta, Atiku ya ziyarci Kano domin karbar Malam Shekarau wanda ya sauya sheka daga jam’iyyar Rabiu Kwankwaso ta NNPP zuwa PDP.