Siyasa
Hukumar INEC ta soke rijistar mutane 1,126,359

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya INEC, ta soke rajistar aƙalla mutane Miliyan Ɗa da dubu ɗari da ashirin da shida da ɗari uku da hamsin da tara.
Hakan na cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter a Litinin ɗin makon nan mai ɗauke da sa hannun babban kwamishinan hukumar ta Festus Okoye.
A cewar sanarwar, hukumar ta INEC, rijistar da ta soke ɗin tana daga cikin sabuwar rajistar mutane Miliyan biyu da dubu ɗari biyar da ashirin da uku da ɗari huɗu da hamsin da takwas da aka yi a tsakanin ranar 28 ga watan Yuni zuwa 14 ga watan Janairun bana 2022.
Haka kuma sanarwar ta ce “Hukumar INEC ta gano cewa wasu mutanen ba su yi rajista dai-dai da tsarin dokakinta ba shi ne dalilin soke rijistar”.