Ya ce: “Za mu horas da jami’an da za su sanya ido kan aikin manyan turawan zaɓe su 17,685 da manyan turawan zaɓe da mataimakan su mutum 707,384, sai Jami’an tattara sakamako su 11,083 da kwararrun Jami’an zaɓe kimanin mutum 12,991 da Jami’an Tsaro kimanin 20,000 da shugabannin kula da cibiyoyin zaɓe 6,009”.
Haka kuma ya ƙara da cewa, sashen su a hukumar ya duƙufa sosai wajen sauke nauyin da ke kansu na tabbatar da ganin dukkan ma’aikatan wucin gadin sun samu kyakkyawan horo da ƙarewa gabanin fara zaɓen.
