Connect with us

Addini

Buhari Ya Bukaci Al’ummar Musulmi Da Su Rika Koyi Da Halayen Annabi Muhammadu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci al’ummar musulmi da su yi koyi da kyawawan dabi’u na Annabi Muhammad sallallahu alaihi wassalam, yana mai cewa, “Hanya mafi kyau da za a girmama shi ita ce a yi koyi da shi,” a cewar wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya sanya wa hannu.

A sakonsa na fatan alheri ga al’ummar musulmi a mauludin murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad, shugaban ya bayyana cewa “ma’aiki ya shahara da tawadi’u da adalci da gaskiya.

A cewar shugaba Buhari, “Manzon Allah ya jawo hankalin mutane zuwa addinin Musulunci ta hanyar misalan gaskiya, rikon amana, adalci, hakuri da juriya.”

Ya bayyana cewa Annabi ya nuna “rayuwa mai ban mamaki ta hakuri a karkashin jagoranci da kuma girmama yarjejeniyoyi da wadanda ba musulmi ba domin zaman lafiya tare.”

Shugaba Buhari ya kara da cewa “Gaskiya yana daya daga cikin manya-manyan dabi’un Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi wa sallam kuma kowane musulmin kirki ya yi koyi da shi.”

Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa, Shugaban ya yi amfani da wannan damar wajen yin kira ga dukkan ‘yan Najeriya da su bi sahun gwamnati a kokarin da ake yi na kawar da rashin tsaro da cin hanci da rashawa; su kara girmama mata da yara da masu karamin karfi; da kuma nuna ƙauna da fahimtar juna.

Ya kuma bukaci ’yan siyasa a wannan kakar zabe da su guji yin amfani da kalaman banza da kalaman batanci, da kuma guje wa al’adun wulakanci da wulakanta abokan hamayya.

Shugaban ya sake yin alkawarin cewa zai tabbatar da zabe mai inganci da gaskiya a 2023.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet