Connect with us

Labarai

‘Bazan Zama Shugaba Har Abada Ba’ Inji Shugaban PDP

Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Sen. Iyorchia Ayu, ya ce an ba shi wa’adin sake kafa jam’iyyar ne ba wai ya wawure dukiyar jam’iyyar ba ko kuma yin sakaci da al’amuran ta.

Ayu ya bayyana haka ne a lokacin da yake tarbar kungiyar zababbun mambobin jam’iyyar da suka kai masa ziyarar a hedikwatar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja.

Ya kara da cewa ya umurci sashin kudi na jam’iyyar da su tabbatar da sabunta asusun kudaden shiga da na kudaden jam’iyyar domin gabatar da su ga kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na kasa a taron tunawa da shekara ta farko na NWC a watan Disamba.

Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa wannan shi ne martaninsa na farko game da tuhumar da ake masa a kafafen yada labarai na cin hanci da rashawa da kuma biyan wasu mambobin kwamitin ayyuka na jam’iyyar na kasa kudade ba bisa ka’ida ba.

Ayu ya ce yana da kura-kurai da yawa a matsayinsa na dan Adam amma sata ba ya cikin su, inda ya yi nuni da cewa a halin yanzu ana gudanar da aiyuka na gaskiya da rikon amana.

A wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Simon Imobo-Tswam ya fitar, ya ce, “ba a kafa jam’iyyar PDP don ta zama ‘yan adawa ba.

”Mun kafa jam’iyyar ne don samun madafun iko da ci gaban kasa kuma aikina na tarihi shi ne na mayar da jam’iyyar kan mulki.

”Ba zan zama shugaba har abada ba, don yanzu burina shi ne in mayar da jam’iyyar kan mulki.” Inji Ayu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahistipobettipobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişjojobetjojobetgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobettipobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet