Labarai
Gwamnatin El-Rufai ta shirya jarrabawa ga Malaman da za ta ɗauka aiki

Hukumar ilimin bai ɗaya ta jihar Kaduna, KADSUBEB ta ce, ta kammala shirin gudanar da jarrabawa ga sababbin malaman makaranta da gwamnatin jihar za ta ɗauka aiki.
Jaridar Solacebase ta rawaitu cewa, hukumar ta sanya ranakun 17 zuwa 28 ga watan nan da muke ciki na Oktoba a matsayin ranakun rubuta jarabawar a shiyyoyi uku da aka ware.
Wata sanarwa da hukumar ta KADSUBEB ta fitar ta ce, a shiyyar kudancin Kaduna, jarabawar zata gudana a makarantar Institute of Information Technology, Kofar Doka, Zaria.
Haka kuma a yankin Kaduna ta tsakiya jarabawar zata gudana ne a Jami’ar jihar Kaduna KASU dake cikin birnin Kaduna, yayin da reshen KASU da ke Kafanchan zai wakilci shiyyar kudancin Kaduna.
Idan za a iya tunawa, Awatan Yulin da ya gabata ne shugaban hukumar ta KADSUBEB, Malam Tijani Abdullah, ya sanar da cewa gwamna Malam Nasiru El-Rufa’i na jihar Kaduna ya umarci hukumar ta ɗauki sababbin malamai har mutum dubu goma.
Haka kuma idan ba a manta ba tun a zangon farko na mulkin gwamna El-Rufai gwamnatinsa ta kori malaman makaranta da dama bayan sun faɗi a jarrabawar gwajin da ta yi musu.