Ministar ta furta hakan ne a taron ƙara wa juna sani kan yadda ake kashe kuɗaɗen haraji wanda ƙungiyar ci gaban tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma ECOWAS ta shirya a birnin tarayya Abuja.

Rahotonni sun bayyana cewa, an kuma shirya taron ne kan bijiro da sabbin tsare-tsare kan yadda za a yi amfani da kuɗaɗen shiga tare da sanya ido kan miƙa bayanai kan kuɗi a tsakaninn mambobin ƙasashen ECOWAS.

Hajiya Zainab Shamsuna Ahmed, wadda ta samu wakilcin babbar darakta a ma’aikatar ta, Fatima Hayatu, ta ce, gwamnati ta damau matuƙa kan yadda ake kashe kuɗaɗen haraji.