Labarai
Da ɗumi-ɗumi: CBN zai sauya fasali wasu daga takardun kuɗi

Babban bankin Najeriya CBN, ya bayyana ƙudurin sa na sauya fasalin takardun kuɗi.
Gwamnan babban bankin, Mista Godwin Emefiele, ne ya sanar da hakan a wata ganawa da manema labarai a Abuja, ya ce sauya fasalin zai shafi kudaden Naira 200, 500, da 1000.
Ya ce an dauki matakin ne domin ganin an shawo kan matsalolin da ake fuskanta kan yadda kudaden da ke yawo a cikin al’umma.
A cewarsa, mafi yawan matsalolin kudade da kasar nan take samu a daga bankuna ne kuma CBN ba za ta bari lamarin ya ci gaba ba da faruwa ba.