Wasu ƴan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne, su sace wasu ɗaliban Jami’ar Nsukka da ke Jihar Enugu a kan hanyarsu ta komawa makarantar bayan jingine yajin aikin ASUU.
Rahotonni sun bayyana cewa lamarin ya faru da misalin ƙarfe 4:00 na yammacin Lahadin da ta gabata a yankin Ƙaramar Hukumar Igbo Etiti.
Haka kuma har lokacin haɗa rahoton babu tabbaci game da yawan ɗaliban da aka sace ɗin.
Sai dai jaridar Premium Times ta ruwaito cewa ƴan bindigar sun shafe tsawon lokaci suna yin garkuwa da matafiya a hanyar tun daga ranar Asabar.
