Connect with us

Labarai

Hukumar KAROTA ta sake cafke direbobin Adaidaita Sahu da take zargi da satar wayoyi

Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA, ta sake cafke wasu matasa biyu masu tuƙa babur ɗin Adaidaita sahu bisa zargin su da sace wayoyin fasinjoji.

Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa ya fitar a yau Alhamis.

Sanarwar ta ruwaito cewa, Waɗanda ake zargi da satar wayoyin sun haɗa da: Ibrahim Sale ɗan unguwar Rijiyar Lemo da Abubakar Salisu mazaunin titin gidan Zoo inda aka same su da satar wayar fasinjan da suka ɗauka Hassan Muhammad Sani.

Sanarwar ta ƙara da cewa, Hassan Muhammad ya shaida wa KAROTA cewa, lokacin da ya tsayar da su ya buƙaci su kai shi Bata daga shatale-talen gatar Dangi, sai dai, bayan sun ɗauke masa wayar sai suka ce ba inda ya bayyana musu za su je ba.

Hassan Muhammad ya kara da cewa bayan da ya sauka ne sai ya fahimci sun ɗauke masa, a inda ya nemi taimakon jami’an KAROTA da ke aiki a wannan wuri.

Haka kuma ta cikin sanarwar jami’in ya ƙara da cewa, Bayan da hukumar KAROTA ta cafke matasan, sun bayyana mata cewa sun shafe fiye da shekara guda suna aikata wannan mummunar ta’adar da babur ɗin Adaidaita Sahu mai lambar KAROTA KRY 1539

Sanarwar ta kuma ce, Hukumar ta miƙa matasan ga rundunar ƴan sanda ta jihar Kano domin faɗaɗa bincike tare da gurfanar da su a gaban kotu.

“Lokacin da Hukumar ta kama su ta sami wayoyi iri daban-daban a hannunsu tare da nau’in kayan shaye-shaye” , a cewar sanarwar

“Shugaban KAROTA, Baffa Babba Ɗan’agundi na ƙara kira ga al’umma da su ci gaba da sanya ido a duk lokacin da za su hau babur ɗin Adaidaita Sahu tare da lura da koriyar lambar jiki da irin mutanen da suke ciki domin guje wa faɗawa hannun ɓata gari”, a cewar Nabilusi.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet