Labarai
‘Yan Sanda Sun Ceto Mutane 21 Da Aka yi Garkuwa Da Su

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina a ranar Juma’ar na ta ceto akalla mutane 21 da aka yi garkuwa da su da suka hada da mata 15 da yara shida a karamar hukumar Dutsinma ta jihar.
An ceto wadanda lamarin ya rutsa da su ne da misalin karfe 04:30 na dare, bayan da rundunar ‘yan sandan ta samu kiran gaggawa cewa ‘yan ta’addan da yawa a kan babura, inda suka yi ta harbe-harbe da bindigogi kirar AK 47 kai-tsaye, suka kai hari a kauyukan Buraji da Sabon Sara.
Bayan samun labarin, Kwamandan yankin Dutsinma, ACP Mohammad Makama, ya jagoranci tawagar ‘yan sanda masu dabara, inda suka tare hanyoyin fita a kauyen Gandun Sarki, inda suka yi artabu da muggan makamai tare da samun nasarar ceto duk wadanda abin ya shafa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Gambo Isah a wata sanarwa da ya fitar, ya ce an kashe ‘yan ta’adda da dama, wasu kuma sun tsere da raunukan harbin bindiga.
Ya kara da cewa har yanzu tawagar jami’an na ci gaba da aiki a yankin da nufin zakulo gawarwakinsu tare da kamo ‘yan ta’addan da suka jikkata yayin da ake ci gaba da bincike.