Uncategorized
Dan wasan Barcelona Pique ya sanar da yin ritaya

Dan wasan bayan kungiyar kwallon kafar Barcelona Gerard Pique ya bayyana cewa lokaci ya yi da zai kawo karshen taka leda.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafin sa na twitter, dan wasan mai shekaru 35 ya ce wasan da kungiyar sa za ta yi da Almeria a ranar Asabar a filin wasa na Camp Nou ne zai kasance wasan sa na karshe.
Pique ya sanu nasarar lashe kofin zakarun nahiyar Turai 4 uku daga ciki da kungiyar Barcelona, sannan kuma ya na cikin tawagar kungiyar kwallon kafar Spain da ta lashe kofin duniya a shekarar 2010 da kuma na Turai a shekarar 201
- A kalaman sa da ya yi ya ce “babu wata kungiya bayan Barca”
Zan za mo mai goyon bayan kungiyar, kuma zan gadar da soyayyar kungiyar Barca ga dana.”
Pique na dan shekara 10 ya koma makarantar horas da yara kwallon kafa ta Manchester United a shekarar 2004, inda a shekarar 2008 ya lashe kofin zakarun nahiyar Turai na farko da kungiyar karkashin jagorancin Alex Ferguson.
Bayan da ya da wo Barcelona, ya lashe kofin La liga 8 da Copas del Ray 7, da kuma kofin zakarun Turai a shekarar 2009 da 2011 da kuma 2015.