Labarai
Mu cigaba da taimakon juna da saka tsoron Allah a dukkanin al’amuranmu- Sarkin Kano

Mai Martaba Sarki Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR NCOL ya tunatar da al’uma su cigaba da kasancewa masu tsoron Allah a zahirinsu da badininsu da kasancewa masu kaunar juna da kuma kyautata taimakon juna.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci hakan ne a wajan taron Maukibin Qadiriyya na bana Karo na 72 da Khalifan darikar Qadiriyya na Africa Sheikh Qaribullahi Sheikh Nasiru Kabara ya shirya kuma aka gudanar a filin taron Kanzul Muɗalsam dake kan titin zuwa Katsina, a cikin birnin Kano.
Mai Martaba Sarkin ya bukaci al’umma su cigaba da yin addu’oi da tausayawa masu rauni dake cikin al’uma.
Yayi Kira ga waɗanda Allah ya bawa shugabancin al’umma su dinga saurare da bincike ta sahihiyar hanya domin sanin halin da suke ciki don taimaka musu bisa la’akari da yanayin tsaro da ake fuskanta.
Sakataren Yaɗa labarai na Masarautar Abubakar Balarabe Ƙofar Na’isa ya ce, Aminu Ado Bayero CFR ya godewa Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jihar Kano bisa yadda suka bayar da kyakkyawan tsaro a lokacin gudanar da taron.
Daga bisani ya godewa Malamai da Limamai bisa yadda suke gudanar da addu’oi domin samun zaman lafiya a jihar Kano da kasa baki daya.