Rundunar ƴan sandan jihar Katsina, ta ce, ƴan bindiga sun saki wasu matasa su ashirin da ɗaya waɗanda suka yi garkuwa da su a garin Mairuwa da ke yankin ƙaramar hukumar Faskari ta jihar.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar SP Gambo Isa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin jiya Asabar.
Sanarwar ta ce, matasan ƴan tsakanin shekaru goma sha shida zuwa ashirin da ɗaya ne inda ƴan bindigar suka yi garkuwa da su a gona kwanaki biyar da suka gabata.
Sai dai ta cikin sanarwar rundunar ba ta bayyana ko an biya kudin fansa ba gabanin l sakin nasu.
