Connect with us

Labarai

EFCC Ta Cafke Tsohon Kwamishinan Gwamnan Jigawa A Wani Sumame

Yayin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ke kara zage damtse wajen gudanar da ayyuka gabanin zabukan 2023, wata tawaga ta musamman a hukumar ta afkawa jihar Jigawa tare da yi izo keyar tsohon kwamishinan al’amuran kananan hukumomi, Honarabul Aminu Ahmed Kanta.

Kanta ya taba rike mukamin kwamishinan al’amuran kananan hukumomi, kwamishinan kasa da tsare-tsare da kuma mai ba da shawara na musamman kan harkokin siyasa a zamanin gwamnatin gwamna mai ci Muhammad Badaru Abubakar a lokuta daban-daban.

Jaridar LEADERSHIP ta tattaro tsohon Kwamishinan, wanda aka cafko shi a ranar Litinin, an kai shi Abuja domin yi masa tambayoyi.

Kanta, wanda makusancin siyasa ne ga Gwamna Badaru a halin yanzu dan takarar jam’iyyar (APC) ne a mazabar Garki da Babura ta tarayya a jihar a zaben 2023.

Duk da cewa har yanzu ba a bayyana dalilan da suka sa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kama shi ba amma hakan ba zai rasa nasaba da shugabancinsa a ofishin alakarsa da wasu ‘yan siyasa a jihar ba.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet