Rahotonni sun bayyana cewa hatsarin ya ritsa da motar bus ɗin ne ƙirar Toyota Hummer da wata mota ƙirar Hyundai Jeep
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, motar Bus ɗin mai lamba GML 102 TA mallakin kamfanin Kano line ne kuma tana dawowa ne daga garin Gombe lokacin da ta yi taho mugama da motar kirar Jeep da misalin karfe 7.30 na daren ranar lahadi.
Shugaban hukumar kare abkuwar hadurra ta kasa reshen jihar Kano, Zubairu Mayo ya shaidawa jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo cewa, jami’an hukumar sun Isa wajen da hatsarin ya faru ne dake kauyen Rege ‘yan tukwane da karfe 7.40.
Ya ce Fasinjoji 13 sun kone kurmus a wajen yayin da wasu 7 suka jikkata
Ko a jiya Litinin guda daga cikin fasinjojin mace ta rasu a asibitin koyarwa na Aminu Kano.