Labarai
Shugaban Kasa Buhari Ya Amince Da karawa Alkalai Albashi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince tare da ba da umarnin a dauki matakin gaggawa wajen aiwatar da shirin inganta albashi da jin dadin ma’aikatan shari’a.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a ranar Juma’ar nan, a wajen bikin kaddamar da Nabo Graham-Douglass Campus na makarantar koyon aikin shari’a ta Kasa da ke Fatakwal ga majalisar ilimin shari’a.
Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, SAN ne ya wakilci Shugaban kasa Muhammadu Buhari a wajen taron.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Dr. Umar Jibrilu Gwandu, mataimakin na musamman kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a, a ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a ya raba wa manema labarai a ranar Juma’a.
A cewar sanarwar, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci shugaban hukumar tattara kudaden shiga da rabon kudi da kuma babban lauyan gwamnatin tarayya da kuma ministan shari’a da su gaggauta fara daukar matakan tabbatarwa da aiwatar da shirin inganta albashi da walwala ga ma’aikatan shari’a a kasa.
‘’Shugaban ya ce wannan da wasu tsare-tsare da dama, an yi niyya ne da nufin karfafa karfi da ‘yancin kai na bangaren shari’a, wanda ya ce ya kasance ginshikin karfi da kwanciyar hankali ga dimokradiyyar kasar.