Connect with us

Labarai

Sanata Shehu Sani Ya Zargi Gwamnatin Buhari Da Jefa Yan Najeriya Miliyan 133 Cikin Talauci

Sanata Shehu Sani ya caccaki gwamnati mai ci da kasa fitar da ‘yan Najeriya miliyan daya daga kangin talauci a maimakon haka ta jefa miliyan 133 cikin matsanancin talauci.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana shirin gwamnati na fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci nan da shekarar 2030.

Babbar Sakatariyar ma’aikatar kwadago da samar da ayyukan yi, Misis Kachollum Daju, ta shaida wa manema labarai a watan Satumba cewa Gwamnatin Tarayya ta yi shirin daukar matakin, idan masu ruwa da tsaki suka taka rawar da ta kamata.

Amma Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta sanar a ranar Alhamis cewa adadin ‘yan Najeriya da ke fama da talauci ya haura sama da miliyan 133, wanda ke wakiltar kashi 63 cikin 100 na al’ummar kasar.

Da yake mayar da martani kan lamarin, Sani ta shafinsa na Twitter ya ce gwamnati ta jefa ‘yan Najeriya miliyan 133 cikin talauci a bisa rahotan hukuma.

Ya ce “Sun yi alkawarin fitar da mutane miliyan dari daga kangin talauci; yanzu a hukumance sun jefa mutane miliyan dari da talatin da uku cikin matsanancin talauci.”

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetRadissonbetsweet bonanzasweet bonanzapadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetholiganbetholiganbetholiganbetmarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetcasibomcasibomcasibomholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişgrandpashabetholiganbetholiganbetgrandpashabetcasinolevantimajbetsekabetjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabetTürkiyenin Casino Sitelerivdcasinograndpashabetgrandpashabet girişGrandpashabetsahabetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetmatbetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobetjojobet