Labarai
Za mu ɗaukaka ƙara kan shari’ar Babachir- EFCC

Hukumar EFCC yaƙi da cin hanci da rashawa ta ce, za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin da kotu ta yi wankewa tare da sallamar tsohon Sakatare Gwamnatin Tarayya Babachir David Lawal daga zargin almundahanar kuɗin nome ciyawa.
Hukumar ta ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter mai ɗauke da sa hannun jami’intama yaɗa labarai Wilson Uwujaran.
EFCC ta ce, tana shirin karɓar kwafin shari’ar da zimmar ɗaukaka ƙara.
A jiya Juma’a ne Babbar kotun tarayya ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Charles Agbaza ta wanke Babachir Lawal da wasu mutane biyar daga zargin badaƙalar kuɗi naira miliyan ɗari biyar da arba’in da huɗu waɗanda aka tanada don gyara sansanonin ƴan gudun hijira a yankin Arewa maso gabas.
Mai Sharia’a Charles Agbaza ya ce babu wani abu da ya nuna cewa Babachir yana da laifi a cikin bayanan da shaidu goma sha ɗaya da EFCC ta gabatar suka bayar.