Connect with us

Kasuwanci

Da ɗumi-dumi: Gwamnatin Kano ta haramta wa direbobin Adaidaita Sahu bin manyan titina

Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ta haramta wa direbobin baburan Adaidaita Sahu bin manyan Titinan jihar.

Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa mai ɗauke da kwanan watan yau Talata 29 ga watan Nuwamba wadda jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA Nabilusu Abubakar Kofar Nai’sa ya aiko wa Kakakihausa.

Sanarwar ta ta ce, Gwamnatin jihar Kano ta hannun Hukumar kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa KAROTA ta haramta wa matuƙa Baburin Adaidaita Sahu min manyan titinan daga gobe Laraba 30 ga watan Nuwamba, 2022.

“Gwamnatin ta ɗauki matakin ne bayan da ta samar da manyan motocin da za su dinga ɗaukar al’umma a titinan da aka haramtawa yan Adaidaita Sahun,” a cewar Sanarwar.

Haka kuma, Sanarwar ta bayyana cewa an haramta wa direbobin baburan Adaidaita Sahun bin titinan Amadu Bello zuwa mahaɗar Munduɓawa zuwa Gazawa da titin Tal’udu zuwa Gwarzo.

Gwamnatin ta bayyana cewa ta tanadi manyan motocin sufuri domin sauƙaƙawa al’umma bin waɗannan hanyoyi.

Sanarwar ta kuma ƙara da cewa, Gwamnatin jihar Kano za ta sanar da ranar da direbobin Adaidaita Sahun za su daina bin wasu manyan titinan da zarar ta samar da ababen hawan da al’umma za su yi amfani da su a waɗannan hanyoyi.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet