Connect with us

Labarai

2023: Tinubu Ya Kalubalanci Shirin INEC Na Amfani Da Na’urar BVAS

 

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya bayyana rashin amincewa da matakin da hukumar zabe ta kasa ta dauka na amfani da na’urar tantance masu kada kuri’a (BVAS) da tura sakamakon zabe ta shafin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC Results Viewing Portal) a zaben 2023.

“Har yanzu INEC ba ta tabbatar mana da lokacin wannan zabe ba da za ta yi amfani da na’urar watsa sakamoko, ta fasahar da zata yi amfani da ita don tantancewa da jimillar kuri’u abin dogaro ne, abin dogaro da kuma tabbatar da tsarin dimokuradiyyar mu kafin mu gabatar da wani abu mai sarkakiya”

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a cibiyar Chatham House da ke birnin Landan a wani bangare na dabarun bayyana shirye-shiryensa na tsaro, tattalin arziki da kuma manufofin kasashen waje a Burtaniya.

Sabon adawar da Tinubu ya yi kan amfani da fasahar kada kuri’a ya karfafa matsayin jam’iyya mai mulki, wadda tun da farko ta yi ikirarin cewa har yanzu Najeriya ba ta kai ga yin amfani da irin wannan fasahar ba a zaben 2023.

Da yake karin haske a gaban masu sauraro daban-daban a dandalin tattaunawa na Burtaniya, Mista Tinubu ya ce yana daya daga cikin ‘yan siyasa a Najeriya a yanzu da suka rasa kwarin gwiwa kan tsarin zaben kasar tare da bullo da sabbin fasahohin gabanin zabe.

“Har yanzu muna rasa kwarin gwiwa kan tsarin dimokuradiyya da na zabe,” in ji shi.

INEC ta dage cewa babu gudu babu ja da baya kan tura amfani fasahar wajen gudanar a zaben 2023.

Mahmud Yakubu, shugaban hukumar zaben ya ce bullo da fasahar BVAS da IREv, na’urar tattara sakamakon zabe cikin lokaci, domin tabbatar da an gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci.

A yayin da ake zargin wasu ’yan siyasa a kasar nan kwanan nan na yin galaba kan hukumar zabe ta janye amfani da BVAS tare da komawa amfani da takardun fom din wajen tantance masu kada kuri’a a zaben badi, ‘yan Najeriya da dama sun rungumi fasahar kuma yayi gargadin cewa watsi da shi na iya haifar da matsala.

Bayanan Mista Tinubu na zuwa ne kasa da watanni uku gabanin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin kasar da aka shirya gudanarwa a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

Za a gudanar da zaben gwamnoni da na yan majalisar jihohi makonni biyu baya a ranar 11 ga watan Maris.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet