Labarai
Hukumar INEC Ta Bayyana Lokacin Karbar Katunan Zabe A Kano

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC) ta sanar da ranar Litinin 12 ga watan Disambar 2022 zuwa Lahadi 22 ga watan Janairu, 2023 a matsayin ranar da za a gudanar da tattarawa da karbar katin zabe PVC a kananan hukumomi 44 na jihar.
SOLACEBASE ta ruwaito cewa Hukumar ta ce za ta kuma karkasa tarin katin na PVC zuwa wuraren rajista 484 daga ranar Juma’a 6 zuwa Lahadi 22 ga watan Janairun 2023.
Wata sanarwa da shugaban sashen wayar da kan masu kada kuri’a na hukumar INEC, a ofishin Kano, A.A Maulud ya fitar a ranar Talata ya ce wadanda ba su iya karbar katin zabe na PVC a ofisohin hukumar na kananan hukumomin na jihar za su iya yin hakan a wuraren yin rajista.
“Yana da kyau a lura cewa bayan 15 ga watan Janairu, 2023, za a mayar da aikin zuwa kananan hukumomin INEC na jihar har zuwa ranar 22 ga watan Janairu, 2023,” in ji sanarwar.
“Don haka ina kira ga duk wadanda suka cancanta kuma masu cancanta da suka yi rajista, ko canja wuri ko kuma suka sake inganta PVC ɗin su a cikin CVR na ƙarshe daga Janairu 2021 zuwa Yuni 2022 da su fito su karɓi katin su na zabe PVC daga karfe 9.00 na safe zuwa 3.00 na rana kowace rana, har da Asabar da Lahadi.
‘’Haka zalika, ya kamata duk masu ruwa da tsaki su taimaka wa hukumar wajen sanar da jama’a wannan ci gaba’’.