Labarai
‘Yarsu Ta Cinna Musu Wuta Bayan Ta Hada Musu Liyafa – ‘Yan sanda

Rundunar ‘yan sanda a jihar Legas ta fara gudanar da bincike kan halin da ake ciki game da safarar miyagun kwayoyi tare da kona wani dattijo mai shekaru 85 da matarsa mai shekaru 80 da diyarsu mai shekaru 52 da haihuwa ta yi.
An tattaro cewa wata tsohuwa mai shekaru 52 mai suna Aleremolen Izokpu ta hadawa mahaifinta mai shekaru 85 mai suna Pa Michael Izokou da matarsa Priscilla ‘yar shekara 80 liyafa ta banka musu wuta.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Laraba a rukunin gine-gine na Gate Estate da ke unguwar Lusada a Okokomaiko, a kan hanyar Legas zuwa Badagry.
A cewarsa, an tabbatar da mutuwar dattijon a asibitin da aka kai su, yayin da matar ta kasance a sume.
Mista Hundeyin ya ce: “Bayanan da aka samu daga baturen yan sanda na yankin DPO Okokomaiko sun nuna cewa a ranar 01/12/22 da misalin karfe 09:00 ne wani ya kawo rahoto a tashar cewa a ranar 30/11/22 da misalin karfe 15:00 na safe ya samu waya. Wata kanwarsa mai suna Osemudiame Izokpu ta ce babbar yarsu mai suna Aleromolen mai shekaru 52 ta baiwa iyayensu miyagun kwayoyi da wani Micheal Izokou mai shekaru 85 da kuma Priscilla Izokpu mai shekaru 80 sannan ta banka musu wuta a lokacin da suke barci.”
“Jami’an bincike sun ziyarci wurin. An kuma ziyarci asibitin inda aka duba wadanda suka jikkata da gawar, aka dauki hotuna tare da ajiye gawar a dakin ajiye gawa na Asibitin Badagry.”
Mista Hundeyin ya kuma bayyana cewa, an kara zage damtse wajen cafke wanda ake zargi bayan ta gudu.
Jaridar DailyNigerian ta rawaito cewa Daya daga cikin ‘yan’uwan wanda ake zargin Akugbe Izokou ne ya kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda bayan daya daga cikin kanwarsu ta sanar da shi ta wayar tarho.