Labarai
2023: Wata Babbar Kotu Ta Rushe Duk Zabukan Fitar Da Gwani Na Jam’iyyar PDP

A jiya ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta soke zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP da aka gudanar a jihar Ebonyi wanda ya fitar da ‘yan takarar majalisar dokokin jiha da na majalisar dokoki ta kasa da kuma na Gwamna a zaben 2023 a jihar.
Mai shari’a Binta Nyako ta umurci jam’iyyar PDP da ta gudanar da sabon taro a Ebonyi domin zaben ‘yan takararta cikin kwanaki 14.
Mai shari’a Nyarko ta kuma umurci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), da ta sanya ido a kan sabbin zaɓen da jam’iyyar PDP za ta gudanar.
Hukuncin ya biyo bayan karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1319/2021, wanda Mista Okoroafor Tochukwu Okorie ya shigar a kan PDP da INEC.
Kotun ta amince da lauyan mai kara, Okoro Mkemakolam, cewa zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP da aka soke a Ebonyi an gudanar da shi ne bisa rashin bin umarnin kotun daukaka kara, tare da dakatar da aiwatar da hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke, wadda ta bayyana Joseph Sila Onu a matsayin shugaban jam’iyyar na jihar Ebonyi.
Mai shari’a Ahmed Mohammed na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya yanke hukunci a ranar 13 ga Afrilu, 2022, ya amince da Joseph Silas Onu a matsayin sahihan shugaban jam’iyyar PDP na jihar Ebonyi.
Da bai gamsu da hukuncin ba, Okoroafor Okorie ta hanyar Okoro ya garzaya kotun daukaka kara na Abuja don yin watsi da hukuncin da karamar kotun ta yanke.
Mai shigar da kara ya biyo bayan ƙarar da bukatar a dakatar da aiwatar da hukuncin da babbar kotun tarayya.
Musamman kotun daukaka kara a ranar 23 ga watan Mayu, ta bayar da umarnin dakatar da aiwatar da hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke, tare da bayar da umarnin a mayar da dukkan bangarorin kan matsayinsu.
Sai dai duk da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke da kuma shigar da umarnin kotun daukaka kara da aka yi wa PDP, wacce ita ma jam’iyyar ce ta daukaka kara, PDP ta ci gaba da amincewa da Onu a matsayin shugabanta na jiha, bisa rashin bin umarnin da aka ce na jam’iyyar PDP. Kotun daukaka kara.
Mai shigar da karar ya roki kotun da ta yi watsi da matakin da PDP ta dauka na rashin bin umarnin kotun.