Labarai
Yanzu-yanzu: Majalisar Wakilai Ta Yi Sammacin Gwamnan Babban Bankin Kasa CBN

Majalisar wakilai ta bukaci babban bankin Kasa CBN da ya dakatar da aiwatar da sabuwar manufarsa ta cire kudaden da aka shirya gudanarwa a ranar 9 ga watan Janairun 2023 har sai an cika sharuddan dokar da ta kafa bankin.
Hakazalika majalisar ta kuma gayyaci gwamnan babban bankin CBN Godwin Emefiele kamar yadda dokar babban bankin kasar ta tanada domin ya yiwa majalisar bayani kan manufofin bankin da dama a kwanakin baya.
An dai fusata ne a zauren majalisar a ranar Alhamis din nan yayin da ‘yan majalisar ke yin Allah wadai da sabuwar manufar kayyade cire kudaden, suna masu cewa hakan zai yi matukar shafar kananan ‘yan kasuwa da tattalin arziki tunda akasarin al’ummomin karkara ba su da damar yin ajiya a banki.
Jaridar Solacebace ta rawaito cewa, Sai dai kuma bayan wani batu da Mark Gbillah ya gabatar kan tanade-tanaden dokar babban bankin kasar, majalisar ta umurci Gwamnan CBN da ya gurfana gaban majalisar a ranar Alhamis 15 ga watan Disambar 2022 domin yi wa majalisar bayani kan dalilin da ya sa a tsayar da manufar.