Labarai
Yan Majalisar Wakilai Sun Raina Kason Da Aka Ware Musu A Kasafin 2023

Majalisar wakilai ta tarayya ta koka kan yadda kasafin kudin majalisar ya gaza.
Kakakin Majalisar Wakilan, Benjamin Kalu, ya ce Majalisar ba za ta iya yin aiki yadda ya kamata ba, idan har za a tafi a wannan kasafin kudin da aka ware mata.
Kalu ya bayyana hakan ne a wajen bikin karramawar karshen shekara da kungiyar ‘yan jaridu ta majalisar wakilai ta yi a Abuja a karshen makon da ya gabata inda ya karbi lambar yabo ta babban mai magana da yawun majalisar.
Kalu ya yabawa kungiyar ‘yan jarida bisa kokarinta na karfafa dimokuradiyya.
Ya ce rundunar ta samar da kwanciyar hankali ga martabar majalisar dokokin kasar.
Ya kuma ce ‘yan jarida ba sa samun abin da ya dace don haka ya kamata a kara kaimi wajen kula da su.