Labarai
Wata Kotu Ta Dakatar Da Hukumar DSS Daga Kama Gwamnan CBN, Emefiele

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta ki amincewa da bukatar da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta shigar na kama gwamnan babban bankin Kasa (CBN) Godwin Emefiele tare da tsare shi.
Da yake kin amincewa da bukatar parte – wanda mai nema ya shigar ba tare da wanda ake kara ba – Mai shari’a John Tsoho, babban alkalin kotun, ya ce hukumar ta DSS ba ta bayar da wata kwakkwarar hujja da za ta tabbatar da ikirarin da ta ke yi na cewa Emefiele na da hannu wajen bayar da kudaden ta’addanci da kuma laifukan tattalin arziki.
Majiyoyi a babbar kotun sun ce alkalin ya ce ya kamata a ba shi tabbaci idan akwai wata hujja da ke tabbatar da zargin da ake yi a cikin takardar mai lamba FHC/ABJ/CS/2255/2022.
“Alkalin mai girma ya kuma yi mamakin dalilin da ya sa aka sanya sunan wanda ake kara a matsayin ‘Godwin Emefiele’ ba tare da bayyana cewa shi mutum daya ne da gwamnan CBN ba, babban jami’in gwamnati wanda ke da matsayi mai matukar muhimmanci,” inji majiyar ya shaida wa TheCable.
Kotun ta ce kamata ya yi a rika bin irin wannan bukata da amincewar shugaban kasa saboda babbar illar da ke tattare da tattalin arzikin Najeriya idan aka kama gwamnan CBN aka tsare shi.
Akwai kuma ra’ayoyin cewa yunkurin kame Emefiele na iya zama na siyasa duba da irin tasirin da sake fasalin kudin Naira da kuma takaita fitar da kudade ka iya haifarwa wajen sayen kuri’u a zaben 2023.
Wasu ‘yan siyasa da dama sun koka da cewa wai an yi masu tsaurin ra’ayi ne a kan sake fasalin kudin Naira amma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bai wa Emefiele cikakken goyon bayansa kan wannan manufa.
Jaridar SOLACEBASE ta ruwaito cewa gamayyar kungiyoyin farar hula (CSOs) a ranar Litinin sun yi zargin cewa hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta kammala shirin kamawa tare da tsare gwamnan CBN, Godwin Emefiele.
Shugaban gamayyar kungiyoyin, Tochukwu Ohazuruike, ya ce hukumar DSS na shirin tsige gwamnan CBN, Godwin Emefiele.