Addini
NAHCON Ta Samu Naira Miliyan 107 Da Aka Dawowa Da Alhazai Daga Saudiyya

Hukumar jin dadin alhazai ta Kasa NAHCON a ranar Talata ta ce ta samu maido da kudi SR542,033 (Naira 107,864,567) daga kasar Saudiyya kan rashin abinci da kamfanonin Mutawwif suka yi wa maniyyata daga kasashen Afirka da ba na Larabawa ba a aikin hajjin 2022.
Mutawwif kamfanoni ne na Saudiyya da ke da alhakin masauki da sufuri da ciyar da mahajjatan Najeriya da sauran kasashen Afirka a Mina da Arafat a lokacin aikin hajji.
An mayar da kudaden ne saboda korafe-korafen rashin abinci da ake bai wa mahajjata a lokacin aikin.
A cikin wata sanarwa da NAHCON ta fitar, ta ce ci gaban ya biyo bayan wasiku ne da ta aika wa kamfanin da aka kulla a lokacin aikin hajjin.
“A cikin wata wasika mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin gudanarwa na hukumar, Dakta Ahmad Bin Abbas Sindi, zuwa ga shugaban hukumar, Zikirullah Hassan, ta bayyana cewa an mayar da kudaden ne saboda rashin ingancin ayyuka da kuma domin kula da dangantakar kasa tsakanin hukumar, an cire kudin S R542, 033 daga adadin kwangilar ciyar da Masha’ir.”
A nasa bangaren, shugaban NAHCON, ya ce ci gaban da aka samu ya yi matukar bada farin ciki, domin ya tabbatar da irin jajircewar da hukumar ta yi na gyara kura-kurai da alhazan Nijeriya a lokacin aikin Hajji, musamman a tsarin ciyar da abinci da ingancin ayyukan da ake yi a lokacin.
“Ina so in godewa takwarorina na Mutawwifs saboda wannan rawar da suka taka wajen ganin sun dawo da kudaden da aka biya don ayyukan da ba a yi ba ko kuma ba a kai su ba,” in ji shi.
Da aka tuntubi mataimakin daraktan yada labaraina NAHCON, Mousa Ubandawaki kan yadda za a raba kudaden, ya ce har yanzu hukumar ba ta karbi kudaden ba.