Connect with us

Kasuwanci

CBN Ya Kara Yawan Kudi Da Kamfani Da Mutum 1 Zai Iya Cirewa A Mako

 

Babban bankin Kasa (CBN) ya koka kan matsin lamba daga ‘yan Najeriya da dama da ‘yan majalisar dokoki yayin da ya sanar da sake duba umarninsa na takaita fitar da kudade.

Yanzu haka dai daidaikun mutane na iya fitar da tsabar kudi Naira 500,000 duk mako kuma kamfanoni yanzu za su iya fitar da tsabar kudi har Naira miliyan 5 a duk wuraren cirar kudi na (ATM) da (POS).

“Mafi girman iyaka na sati-sati don fitar da tsabar kuɗi a duk tashoshi na daidaikun mutane da kamfanoni zai zama Naira 500,000.00 da Naira 5,000,000.00 bi da bi,” babban bankin ya ce a wata takardar da aka fitar a ranar Laraba mai dauke da sa hannun Daraktan sa ido na Bankin, Haruna Mustafa.

Umarnin zai fara aiki ne daga ranar 9 ga watan Janairu, 2023, babban bankin ya ci gaba da cewa, an daidaita tsarin ne bisa amsa da aka samu daga masu ruwa da tsaki bayan sanarwar farko da ta yi a ranar 6 ga watan Disambar 2022.

Jaridar Alkiblah ta rawaito cewa A ranar 6 ga watan Disambar 2022 ne CBN ya umarci Bankunan Kudi (DMOs) da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi da su tabbatar da fitar da kudaden da mutane da kamfanoni ke cirewa duk mako bai wuce Naira 100,000 da Naira 500,000 ba.

Haka kuma ta sanya mafi girman cire kudi na yau da kullun ta hanyar ATM da PoS akan Naira 20,000 kuma ta ce adadin Naira 200 da kasa kawai za a loda a cikin ATM.

Babban bankin na CBN ya ce sabuwar manufar ta biyo bayan kaddamar da sabon tsarin kudi na Naira 200, da Naira 500 da kuma Naira 1,000 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi a ranar 23 ga watan Nuwambar 2022.

Umarnin ya haifar da cece-kuce da bacin rai daga miliyoyin ‘yan Najeriya da ‘yan majalisar dokokin kasar da suka ki amincewa da wannan manufa. Da yawa daga cikin ma’aikatan PoS sun ce manufar za ta danne musu ayyukansu tare da kwace musu ayyukan yi yayin da ‘yan siyasa ke cewa manufar kai hari ne kan jam’iyyun adawa gabanin babban zabe na 2023.

Amma babban bankin a ranar Laraba ya kara iyakokin fitar da kudade na mako-mako zuwa Naira 500,000 ga daidaikun mutane da kuma Naira 5m na kamfanoni.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet