Labarai
Wata Kotu Ta Tisa Keyar Wani Matashi Gidan Yari Bisa Lalata Fastar Dan Siyasa

Wata kotun yanki da ke garin Bukuru na jihar Filato, ta yanke wa wani matashi hukuncin ɗaurin shekaru biyu a gidan yari, bisa samun sa da aikata laifin lalata allon kamfe, na ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP atiku abubakar.
Alƙalin kotun, mai shari’a Hycinth Dolnaan ne ya yanke hukuncin, kan zargin haɗa baki da kuma aikata ba daidai ba, inda yace laifin ya saɓawa sassa na 59 da na 313 na kundin laifuka na jihar.
Matashin mai suna Gabriel Orupou ya nemi afuwar kotun, tare da bayyana cewa wasu ne suka sashi lalata allon kamfen ɗin, da nufin zasu bashi kuɗi naira dubu biyu.
Tuni dai sauran mutanen da suka sashi aikata wannan aika-aikar suka ranta ana kare, inda ake cigaba da neman su ruwa a jallo, duba da laifin da suka aikata ya saɓa wa doka.