Labarai
Majalisar Dokokin Jiha Na Shirin Samar Da Dokar Kula Da Mata Da Yara Kyauta A Kano

Majalisar dokokin Kano ta karbi kudiri dake neman yin doka da zata rinka kulawa da mata masu ciki da kananan yara.
Kakaki Hausa Times ta rawaito cewa, makasudin Kudurin shine, don basu kulawa a asibitoci jihar kyauta ba tare da sun biya ba.
Dan majalisa mai wakiltar Rogo, Magaji Dahiru Zarewa, da hadin gwiwar dan majalisa mai wakiltar Takai, Musa Ali Kachako, ne suka gabatar da kudirin yayin zaman majalisar a Talatar nan.
Da yake jawabi a gaban majalisar, Magaji Dahiru Zarewa, ya ce idan aka amince da kudirin ya zama doka zai magance matsalar mace-macen yara da ake samu da kuma kulawa da mata tun daga daukar ciki zuwa haihuwa.
Yanzu haka dai ana ci gaba da samun mutuwar mata masu juna biyu, sakamakon rashin samun kulawar da ta kamata.