Labarai
Buhari Zai Kunyata Masu Shirin Amfani Da Gwamnati Wajan Yin Magudin Zabe — Gwamna Bala

Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya bayyana fatansa na cewa ‘yan siyasar da ke shirin yin magudi a zaben 2023 ba za su yi nasara ba. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a ranar Lahadin da ta gabata a lokacin da ya karbi bakuncin Mambobin kungiyar Kiristocin Jihar Bauchi yayin bikin Kirsimeti a Bauchi.
Gwamna Bala ya bayyana shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin mai adalci, yana mai jaddada cewa shugaban kasar zai cika alkawuran da ya dauka na tabbatar da zabe mai inganci.
Ya bukaci ‘yan Najeriya da su amince da shugaban kasa kuma su yi watsi da wadanda ya bayyana a matsayin masu shakkar “Ikon Al’umma.”
“Akwai masu sayen kuri’u, kuma akwai masu shirin yin magudin zabe ta hanyar amfani da karfin Gwamnatin tarayya amma na san Shugaba Buhari mai adalci ne, kuma ya riga ya tabbatar mana da cewa zai bar jama’a su zabi wanda suke so. ”
“Kada mu damu da duk waɗannan masu shakku da da Ikon Al’umma. Dole ne mu iya hadu tare,” inji shi.