Labarai
Yan Sanda Sun Damke Wani Jami’in Dan Sanda Bisa Laifin Harbe Wata Lauya

Rundunar ‘yan sanda a jihar Legas ta kama wani mataimakin Sufeton ‘yan sanda, ASP, dake aiki a sashin Ajah bisa zargin kashe wata lauya a ranar Kirsimeti.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Benjamin Hundeyin ya tabbatar da faruwar lamarin da kamun a ranar Litinin.
Ya ce an kuma kama wasu ‘yan sanda biyu da ke tare da ASP domin yi musu tambayoyi.
“Wani abin takaici ne kuma abin da za a iya kauce masa. Tuni dai ASP da ya harbe ta da wasu mutane biyu tare da shi aka tsare su.
“Za a kai su sashin binciken manyan laifuka na jihar, da ke Panti, a Yaba, don ci gaba da bincike,” in ji Mista Hundeyin.
Kakakin ya kuma bayyana cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas, Abiodun Alabi, ya tuntubi iyalan mamacin da kuma kungiyar lauyoyin Najeriya kan wannan mumunan lamari.
Mista Hundeyin ya kara da cewa, “Mr Alabi ya ba da tabbacin cewa adalci zai tabbata.”
Kamfanin dillancin labarai na Kasa (NAN) ya tattaro cewa lamarin ya jefa al’umma cikin rudani yayin da dan sandan da ake zargin shi da tawagarsa suka gudu daga wurin nan take.
Jaridar DailyNigerian ta tattaro cewa jami’an ‘yan sanda na Ajah sun kama jami’in tare da tsare shi.
Jaridar Alkiblah ta samu labarin cewa marigayiyar, ‘yar uwarta, da kuma ‘ya’yanta hudu suna dawowa ne daga wajen bikin Kirsimeti a cikin motarsu da misalin karfe 11:00 na safe lokacin da dan sandan ya yi kokarin hana su.
Wata majiya ta ce matar tana kokarin yin juyiwa ne a karkashin gadar Ajah, sai ASP ya harbi motar ta harsashin ya same ta.
“An garzaya da ita asibiti inda aka tabbatar da mutuwarta,” inji majiyar.