Wasu ƴan bindiga a jihar Zamfara, sun sace Kanal Lawal Rabiu Yandoto mai ritaya a kan hanyarsa ta zuwa garin su na Yandoto da ke Karamar Hukumar Tsafe a Jihar.
Rahotonni sun bayyana cewa ɓata garin sun sace shi ne tare da ƴaƴansa biyu tare da ƙarin wasu mutanen.
Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa, ƴan bindigar sun yi wa tsohon Kanal ɗin kwanton ɓauna ne da misalin ƙarfe 6:00 na yamamcin jiya Lahadi.
Haka kuma kafar ta ruwaito cewa an ji ƙarar harbe-harbe a kusa da bakin garin na Yandoto lamarin da ya tilasta wa mutane guje-guje domin tsira.
Haka kuma rahotonni sun bayyana cewar bayan lafawar harbin ne aka gano motar Kanal ɗin babu kowa a cikinta.