Labarai
Bauchi: Mutane 18 sun ƙone a hatsarin mota

Rahotonni daga jihar Bauchi, sun bayyana cewa, mutane goma sha takwas sun ƙone ƙurmus sakamakon wani hatsarin mota da ya ritsa da su a yankin ƙaramar hukumar Toro.
Kwamandan yanki na hukumar kare afkuwar haɗura ta ƙasa FRSC Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da faruwar iftila’in ga manema labarai yana mai cewa hatsarin ya faru ne a ƙauyen Narbodo.
Haka kuma, ya ce, hatsarin ya shafi motar bus ƙirar Toyota Hiace da kuma babbar mota, wadda mutum uku da ke cikinta ba su ji ko ƙwazane ba.
Kwamandan, ya ƙara da cewa, hatsarin ya faru da misalin ƙarfe 4:40 na yamma, kuma jami’an hukumar sun isa wurin cikin minti bakwai da faruwarsa.
Yusuf Abdullahi, ya kuma ɗora alhakin hatsarin kan gudun wuce sa a da ya sanya motocin yin taho mu gama.
wanda ya haddasa motocin biyu suka yi karo da juna.