Labarai
Ba A Sami Rasa Rai Ba A Gobarar Da Ta Tashi A Hedikwatar Yan Sandan Kano – PPRO

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ba a samu asarar rai ba sakamakon gobarar da ta tashi da yammacin ranar Asabar a shedikwatar rundunar.
Jaridar Alkiblah ta rawaito cewa Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan (PPRO), SP Abdullahi Haruna-Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Kano.
“Gobara ta cinye bene na farko na shedikwatar rundunar ‘yan sandan jihar Kano da ke Bompai.
“Ofisoshin da gobarar ta kone sun hada da ofishin Provost, DC hada hadar kudi da ofishin Admin, ofishin AC Admin, ofishinAC ayyuka Operations, ofishin kudi da kakakin hukumar PPRO, da sauransu. Amma bayanan Umurnin suna cikin kulawa.
“Ba a yi asarar rai ba kuma ba a sami rahoton wani rauni ba. Jami’an kashe gobara ne suka shawo kan gobarar,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta ce, mataimakin gwamnan jihar Kano, Dakta Nasiru Gawuna, ya ziyarci wurin da lamarin ya faru, domin jajanta wa ‘yan sanda da babban sufeto Janar na ‘yan sanda (IGP), da mataimakin sufeton AIG na shiyya ta 1 wanda shi ma ya halarci wurin.
“CP Mamman Dauda da jami’an ‘yan sandan Kano, kuma a madadin gwamnatin jihar Kano sun yi alkawarin taimakawa,” in ji sanarwar.
Shi ma a zantawarsa da jaridar Alkiblah kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Alhaji Saminu Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ana ci gaba da bincike kan musabbabin tashin gobarar. (NAN)