Labarai
Wata Motar Ayarin Magoya Bayan PDP Ta Kife Da Mutane Sama Da 70

Wata babbar mota dauke da magoya bayan jam’iyyar PDP sama da 70 ta yi hatsari a jihar Filato, inda mutane da dama suka mutu.
Hatsarin ya afku ne a ranar Asabar a kauyen Jwak da ke gundumar Panyam a karamar hukumar Mangu ta jihar bayan taron jam’iyyar na shiyyar da aka gudanar a Pankshin.
Mista Peter Longsan, jami’in ilimin jama’a na hukumar kiyaye aukuwar hadurra ta kasa (FRSC) a Filato ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN faruwar lamarin a Jos.
Longsan, wanda ya yi alkawarin bayar da karin bayani, ya ce ya zuwa yanzu an tabbatar da mutuwar mutane bakwai.
“Yayin da muke magana, har yanzu ina jiran cikakken rahoto daga mutanen mu da suke wajen, amma ya zuwa yanzu, an ce mana mutane bakwai sun rasa rayukansu.
“An kuma shaida mana cewa sama da mutane saba’in ne a cikin motar da ta yi hatsari a Panyam a Mangu a kan hanyarsu ta komawa Jos,” inji shi.
Jaridar Solacebace ta rawaito cewa Longsan ya ce a halin yanzu wadanda suka jikkata na samun kulawa a wani asibiti da ke garin Mangu.
Mista Caleb Mutfwang, dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a jihar a wata sanarwa da ya fitar, ya jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu, tare da yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa.
Dan takarar ya ce yana ziyartar wadanda abin ya shafa a asibitoci daban-daban domin sanin tsananin halin da suke ciki da kuma matakan da ya kamata a dauka. (NAN)