Labarai
Wasu ‘Yan Makaranta Takwas Sun Mutu Bayan Kifewar Wani Jirgin Kwale-kwale

Wasu yara ‘yan makaranta har guda takwas sun mutu a yankin Bono Gabas ta kasar Ghana bayan da jirgin ruwan da ya kai su makaranta ya kife a tafkin Volta, kamar yadda jami’ai suka tabbatar.
Hukumar kula da iftila’i ta kasar (NADMO) ta shaida wa manema labarai cewa mutane takwas, maza biyar da mata uku ‘yan shekaru biyar zuwa 12, na daga cikin dalibai 20 da ke kan hanyarsu ta zuwa makaranta a unguwar Wayokope da ke fadin tafkin.
Ibrahim Wudonyim, Ko’odinetan hukumar ta NADMO, ya ce rundunar ‘yan sandan ruwa ta hukumar ‘yan sandan kasar Ghana tare da taimakon wasu ‘yan kasar sun gano gawarwakin wadanda suka mutu.
Ana ci gaba da bincike don gano musabbabin hatsarin. (Xinhua/NAN)