Uncategorized
Real Madrid ta fitar da Atletico Madrid daga gasar Copa del Rey

Real Madrid ta kai zagayen wasan kusa da na karshen gasar Copa del Rey, bayan lallasa Atletico Madrid da kwallaye 3-1 a daren jiya Alhamis.
Atletico ce dai ta fara jefa wa Real Madrid kwallon a raga ta hannun dan wasanta Alvaro Morata cikin mituna na 19, sai da kuma aka kai 79 Real ta rama kwallon ta hannun Rodrygo, abinda ya sanya aka tafi karin lokaci na mintuna 30.
Daga bisani ne’ yan wasan Real Karim Benzema da Vinicius Junior suka jefa kwallo guda-guda.
An dai buga wasan ne sa’o’i bayanda kocin Atletico Madrid Diego Simone ya bukaci hukumomin kwallon kafa da su soke batun karin lokacin mituna 30 da ake yi a wasan da ake neman wanda zai yi nasara a cikinsa, inda a maimaikon haka ya ke ganin gara a tafi bugun daga kai sai mai tsaron raga.
A wani labarin kuma, a dai daren na jiya Alhamis, Athletic Bilbao ta lallasa Valencia da kwallaye 3-1 a zaggayen kwata final na gasar Copa del Rey.