Featured
Kotu Ta Bayar Da Umarnin A Kamo Shugaban Jam’iyyar APC Na Kano, Abdullahi Abbas

Wata babbar kotu a jihar Kano ta ba da umarnin a kamo mata shugaban jam’iyyar APC na jihar Abdullahi Abbas.
Jaridar Sahelian Times ta ruwaito cewa, tun da farko wani ne mai suna Mahmoud Lamido ya gurfanar da Abdullahi Abbas ɗin a gaban kotun bisa zarginsa da yi masa barazana ga rayuwarsa da tayar da hankali ta hanyar amfani da kalaman da ba su dace ba.
Haka kuma lauyan Mahmoud Lamido, Bashir Yusuf Muhammad ya bayyanawa kotun cewa Abdullahi Abbas ɗin ya yi barazanar kashe wanda ya ke karewa.
Bashir Yusuf ya ce shugaban jam’iyyar ta APC ya kira Mahmoud Lamido a wayar sadarwa inda ya yi masa barazanar raba shi da rayuwarsa.
A ƙarshe mai shari’a S. A. Amobeda, ya ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 16 ga watan nan na Fabarairu domin cigaba da Shari’ar.