Labarai
Wani Mahaifi Ya Maka Dansa A Gaban Kotu Akan Wasu Kudade

Saboda watsi da shi da kuma rashin dogaro, wani uba dan Najeriya ya kai dansa kara gaban kotun shari’a domin ya dawo masa da zunzurutun kudi Naira miliyan 50 daya nashi don yin kasuwanci.
Mutumin ya bai wa ɗansa makudan kuɗade don gudanar da sana’ar iyali amma ’ya’yansa suka yi watsi da shi.
A gaban kotun, mahaifin yaron ya bayyana matashin a matsayin wanda bai cancanci a amince da shi ba.
Mahaifin yaron dan Najeriya ya maka dansa mai suna Chijioke kara a gaban kotu domin ya mai do masa da naira miliyan 50 da ya ba shi don gudanar da sana’ar kasuwanci ta iyali.
Mahaifinsa ne ya kai Chijioke zuwa kotun shari’a kara . Kotun shari’a shiri ne na kotun gaskiya a Najeriya Alternative Dispute Resolution (ADR) da ake watsawa a gidan talabijin domin sasanta kananan rigingimu kuma Funmilayo Asaolu ce ke shugabantarta.
An raba bidiyo daga kwanan su a kotu akan TikTok kuma mutane da yawa suna magana.
A cikin faifan Bidiyon, alkalin ya koka kan yadda mutane ba sa yaba abin da suke da shi har sai an bata sannan ya ce wa Chijioke cewa mahaifinsa na cikin halin tausayi amma ba ya neman komai.
“A cikin Naira miliyan 50, bari ya fara bani Naira miliyan 20, bai cancanci amanar da uba zai yi wa dansa ba, na ba shi cekin na Naira miliyan N50m, ya je ya kwashe kudin, bari ya mayar da Naira Miliyan N50m.” me yake yi da kud’in?” Mahaifinsa yayi maganar cikin bacin rai da takaici a gaban kotu.
Mutumin ya ce Chijioke ya yi masa wauta kuma baya son shi don gudanar da kasuwanci.
“Shi ya yi na Naira miliyan N1m? Ya samu Naira dubu N100k da kansa? Ni ban yarda da shi ba, bai cancanci nashi kowace amana ba.
“Bana son ka cigaba da tafiyar da kamfanin, ka bani kudi da kayan aikina, ka tafi ka fara sana’ar ka.”
Ya caccaki Chijikoe da fatan zai mutu kuma ya bayyana cewa zuwan kotu ya zama dole a gareshi domin saurayin ya kaucewa kiran da dattawan su suka yi masa kan lamarin.